30 Yuni 2026 - 16:10
Source: ABNA24
A Ci Gaba Da Hare-Haren Isra’ila A Gaza; Falasdinawa 8 Ne Sukai Shahada, Dayawa Sun Jikkata

A daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, hare-hare ta sama da na manyan bindigogi na gwamnatin yahudawa a yankuna daban-daban na wannan zirin a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sun kai ga shahadar aƙalla Falasdinawa 8 da jikkatar wasu da dama.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Bisa ga rahotannin cikin gida, a wani harin ta sama da aka kai a yankin Al-Mawasi a yammacin Khan Yunis, Falasdinawa biyu sun yi shahada kuma mutane 27 suka jikkata. Har ila yau, jiragen yaƙi na gwamnatin yahudawa sun kai hari kan tantunan 'yan gudun hijira a kusa da Jami'ar Al-Aqsa a Khan Yunis, wanda ya kai ga shahadar wata mata da 'yarta mai shekara ɗaya, kuma tantuna da dama sun kone suka lalace.

A wani hari da aka kai a birnin Deir al-Balah a tsakiyar zirin Gaza, Falasdinawa uku, ciki har da wani yaro, sun yi shahada sakamakon bama-bamai da Isra’ila ta jefa a kan taron jama'a, kuma wasu biyar sun jikkata. A lokaci guda, sojojin gwamnatin yahudawa sun ci gaba da aikin lalata gidaje a gabashin birnin Gaza da arewa maso gabashin Khan Yunis, kuma sun ƙara tsananta hare-harensu a yankuna daban-daban na wannan ziri.

………………………..

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha